An hallaka Mayakan Boko haram da dama a jihar Borno


 

Mayakan boko haram da dama ne suka hallaka yayin gumurzu tsakanin su da Sojojin Najeriya a jihar Borno dake shiyar arewa maso gabashin kasar

Rahotanin dake fitowa dga Najeriya sun ce a jiya Assabar Sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin mayakan  kungiyar Boko haram a jihar Borno tare da hallaka 14 daga cikin su.

A bangare guda, mayakan boko haram din sun kai hare-hare da dama kan Sojojin Najeiyan inda suka kashe 5 tare da jikkata wasu 4 daga cikin su.

Daga faras rikicin Boko haram a shekarar 2009 zuwa yanzu a Najeriya, alkaluma sun ce sama da mutane dubu 20 ne suka rasa rayukan su yayin da wasu sama da miliyan biyu da dubu 600 suka rasa mahalinsu.

You may also like