An hallaka ‘yan kunar-bakin-wake uku a Maiduguri


4bk552598c4b3679om_800c450

 

Dakarun tsaron Najeriya sun karyata jita jitan cewa sun dauko sojojin haya a yakin da suke yi da kungiyar boko haram

A wata sanarwa da kakakin sojin Najeriya Birgediya Janar Rabe Abubakar ya fitar a jiya Alhamis ya karyata jita-jitan cewa a kwai Sojojin haya na kasashen waje a cikin jerin Sojojin Najeriya da suke yaki da Kungiyar Boko haram,sannan ya ce Dakarun tsaron kasar nada  karfi da kuma makaman isassu na yakar kungiyar boko haram.

Birgediya Janar Rabe Abubakar ya kara da cewa Sojojin Najeriya ba tare da taimakon Dakarun kasashen waje ba sun samu nasara mai yawa a yakin da suke yi tare da kungiyar Boko haram, dauko sojojin haya na kasashen waje bayan wannan gagarumar nasarar da aka samu abu ne da hankali ba zai dauka ba.

A bangare guda, Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin kasar na cewa an kashe wasu ‘yan kunar-bakin-wake da suka yi yunkuri tayar da bama-bamai da safiyar Juma’a, rahoton ya ce dukkanin maharan uku mata ne, kuma sun yi yunkurin shiga birnin Maiduguri ne amma aka ci lagonsu a unguwar Ummurari da ke wajen birnin.

A cikin ‘yan kwanakin nan kungiyar Boko haram din ta tsananta kai hare-hare a birnin na Maiduguri.

You may also like