A wani sumame da Dakarun hadin gwiwa na kasar Somaliya da na kungiyar tarayar Afirka suka kai wa mayakan Ashabab a kudancin kasar sun samu nasarar hallaka 10 daga cikin su.
Kamfanin dillancin Labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto Shekh Ali babban jami’i a Gwamnatin kasar Somaliya na cewa a jiya Juma’a Dakarun hadin gwiwa na kasar da na kasashen kungiyar tarayyar Afirka sun kai wani sumame kan mayakan kungiyar ta’addancin nan ta Ashabab kusa da garin Bardira na kudancin kasar, inda suka hallaka mayakan kungiyar guda 10 tare da raunana wasu 7 na daban.
Tun bayan janyewar Dakarun tsaron kasar Ethiopia dake kalkashin Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka wato Amison a makun da ya gabata, mayakan kungiyar ta Ashabab suka tsananta kai hare-hare a wasu yankunan kudancin kasar musaman ma yankunan da dakarun kasar Habashan ke kula da tsaron su inda suka sake mamaye wasu daga cikin su.
idan ba a manta ba a shekarar 2015 din da ta gabata ce Dakarun hadin gwiwa na kasar Somaliya da na kungiyar wanzar da zaman lafiya na Amison suka ‘yanto garin Bardira daga mamayar kungiyar ta’addancin nan ta Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar Alka’ida.