Hamas ta gargadi Isra’ila a kan shiga Rafah – DW – 02/11/2024Ko baya ga Hamas din kasashen duniya na ci gaba da kira ga Isra’ila na ta janye daga wannan yunkurin kai hari a yankin na Rafah da dubban Falasdinawa ke neman mafaka.

Sai dai Firaministan Isra’ila Benjamin Nethanyahu ya ce ta haka ne kawai za su kakabe ‘yan kungiyar Hamas, inda ya sha alwashin dakarun sojojinsu za su tabbatar fararen hula basu sami ko wane rauni ba a yayin da ake fiddasu.
 

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu da ke Gaza ta ce ya zuwa yanzu adadin wadanda suka rasa rayuukansu tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da yaki a Gaza ya hauura mutum 28, 000

Yayin da sabbin adadin da aka samu a kasa da sa’o’i 24 sun haura mutum 110, ma’aikatar lafiyar ta kara da cewar sama da fararen hula 67, 000 ne suka jikkata tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba shekarar bara.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like