
Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoto daga jaridar nan mai bin diddigin dukiyar masu kuɗi a duniya, Bloomberg ta ce ga ɗumbin mafi yawan mutanen da suka fi arziƙi a duniya, shekara ta 2022 da ke ban kwana, za a so a manta da ita.
Ta ce a cikin wani rahoto mai taken ƙididdigar biloniyoyi ta Bloomberg dukiyar mutanen da suka fi kuɗi a duniya kusan dala tirliyan ɗaya da biliyan 400 ce ta salwanta.
Masu kuɗin in ji rahoton sun kai yawan 500 kuma asarar da suka yi ba ta kuɗi ba ce kawai.
Ya ce babban abin ciwon kamar yadda abubuwan suka bayyana, duniya ce da kanta ta janyo gawurtacciyar asarar.
Abubuwan da rahoton ya ɗora wa alhakin wannan asarar dukiya sun haɗar da zargin damfarar maƙudan kuɗin kirifto na mai rusasshen kamfanin FTX, Sam Bankman-Fried.
Haka zalika, mummunan yaƙin da Rasha ta ƙaddamar a kan Ukraine ya janyo takunkuman da suka durƙusar da harkokin kasuwanci musamman a tsakanin mashahuran masu kuɗin ƙasar.
Haka wautar Elon Musk in ji rahoton na Bloomberg sabon mai kamfanin Twitter wanda dukiyarsa yanzu ba ta fi dala biliyan 138 ba, ƙasa da abin da ya mallaka a farkon shekarar 2022.
Idan aka haɗa da gagarumin hauhawar farashi da tsauraran matakan manyan bankunan ƙasashe, shekarar 2022 ta kasance wata baƙar ƙaddara ga rukunin biloniyoyin duniya waɗanda dukiyar ta yi matuƙar ƙaruwa a lokacin annobar korona.
Ga mafi yawan masu kuɗi, gwargwadon yawan kuɗin da suka samu a shekarar annobar korona, gwargwadon girman asarar da suka tafka kenan.
Bloomberg ta ce Elon Musk da Jeff Bezos da Changpeng Zhao da Zuckerberg su kaɗai sun yi asarar dala biliyan 392 a cikin tsagwaron dukiyarsu.
Sai dai wani abin ƙarfafa gwiwa shi ne, ba duka aka taru aka zama ɗaya ba ga wani rukuni na masu kuɗin duniya.
Hamshaƙin mai kuɗin nan na ƙasar Indiya Gautam Adani ya zarce Bill Gates da Warren Buffet a jerin masu kuɗin duniya.
Haka zalika, su ma wasu dangin masu kuɗin duniya kamar Kochs da Mars clan, duk sun samu ƙari a cikin dukiyarsu.