Hana al’umma fita zanga-zanga a birnin Khartoum | Labarai | DWA shirin ko ta kwana masu aiko da rahotanni sun ce tun a jiya Laraba titunan birnin Khatoum ke cike makil da sojoji kuma an ayyana yau Alhamis a matsayin ranar hutu.

6 ga watan Afirilu na zama rana mai ciki da tarihi a fage na siyasar Sudan ina da sau biyu sojoji ke hambarar da halastaciyyar gwamnatin farar hula.

A yau ne aka shirya zama domin rattaba hannu a kan yarjejeniyar maida mulki ga gwamnatin farar hula a kasar, sai dai bangaren kungiyoyin fararen hula sun yi kira da a kauracewa wannan zama da ma neman al’umma su fita tituna yin bore.

Sudan dai ta shiga wani hali na rashin tabbas tun bayan da aka hambarar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2021.
 

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like