An Hana Kiwon Dabbobi A Cikin Garin Abuja


 

Ministan babban birnin tarayya Abuja Muhammad Bello, ya sanar da dakatar  da masu kiwon dabbobi a cikin garin da su daina ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Wannan ya biyo bayan korafin da mazauna garin ke yi kan yadda dabbobi ke shiga ko ina.

Ministan ya kaddamar da kwamiti mai wakilai daga kungiyar Miyetti Allah da zai lura da masu irin wannan dabi’un don kawar da aukuwar hakan.

You may also like