- Marubuci, Imran Qureshi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hindi

‘Yan Indiya 16 na cikin matafiya a jirgin ruwa da Najeriya ta ƙwace jirginsu a watan Nuwamba
Ba sabon abu ba ne matafiya su shafe tsawon lokaci ba tare da iyalansu ba a lokutan Kirsimeti da bukukuwa.
Amma wannan karon ya fi zafi ga iyalan Indiyawa 16 matafiya da Najeriya ke tsare da su tun daga watan Nuwamba, lokacin da hukumomi suka ƙwace jirgin ruwansu.
Mutanen, dukkansu maza, na cikin matafiya 26 da ke cikin jirgin mai suna MT Heroic Idun. Sauran ‘yan Sri Lanka ne da Philippines da kuma Poland.
Hukumomin Equatorial Guinea ne suka fara tare jirgin wanda mallakar kamfanin OSM Maritime Group ne na ƙasar Norway a watan Agusta bayan Najeriya ta tsegunta mata cewa akwai yiwuwar matafiyan sun saci ɗanyen mai daga ƙasar.
A wannan makon, Ministan harkokin Wajen Indiya S Jaishanka ya faɗa wa majalisar ƙasar cewa Najeriya ta gabatar da tuhuma a kansu game da “haɗa baki, da kauce wa dokoki, da kuma jigilar man fetur ta ɓarauniyar hanya”.
A ranar 10 da 11 ga watan Janairu ne wata kotu a Najeriya z ata fara sauraron ƙarar tasu.
“Za mu taimaka musu a shari’ar kuma za mu yi duk abin da za mu iya wajen tallafa musu,” a cewar ministan.
Har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta ce komai ba game da mutanen a hukumance.
Bayan wata kusan huɗu, iyalan matafiyan sun bayyana ƙwarin gwiwarsu da fata.
“A baya, mijina ya taɓa yin Kirsimeti a wani waje daban amma bai daɗe kamar haka ba,” kamar yadda Sheethal Milton ta faɗa wa BBC. Mijinta ya shafe shekara fiye da 20 yana tuƙa jirgin ruwa kuma yana aiki ne a matsayin direba a kan jirgin na MT Heroic.
A watan Agusta, matafiyan na kan hanyarsu ta ɗaukar dakon mai daga Equatorial Guinea da Najeriya da zimmar kai shi Rotterdam na ƙasar Holland.
A cewar Sapna Trehan, matar shugaban matafiyan mai suna Tanuj Mehta, an buƙaci jirgin ya bar tashar AKPO a Najeriya bayan hukumomi sun ce ba su san da zuwansa ba.
Matafiyan sun shafe watanni ba tare da ganin iyalansu ba
Bayan jirgin ya bar Guinea, sai wani jirgin ya biyo shi yana iƙirarin cewa na Sojan Ruwan Najeriya ne, kamar yadda Trehan ya faɗa wa matarsa, kuma da zuwansu aka kama su a can.
Matar Trehan ta ce jirgin nasu bai iya tantance jirgin ruwan sojan ba saboda duhu, abin da ya sa suka zaci na ‘yan fashin teku ne.
Yayin wani taron manema labarai ranar 15 ga wtaan Disamba, wani jami’in sojan ruwan Najeriya ya ce “baya ga guje wa kamu ta hanyar doka, direban jirgin ya kira ofishin kula da ruwa na duniya (International Maritime Bureau) da iƙirarin ƙarya cewa ‘yan fashi ne suka kawo musu hari”.
Jami’in ya kuma ce akwai yiwuwar jirgin ya karya dokar fasa-ƙwauri da kuma shige da fice.
Lokacin da aka tsare jirgin a Equatorial Guinea, fasinjojinsa da yawa sun ɗauki bidiyo tare da kiran iyalansu don neman ɗauki. Sun kuma bayyana fargabar kai su Najeriya saboda abin da suka kira irin yadda wasu matuƙa jirage suka ƙare a ƙasar.
A 2021, Najeriya ta saki wani jirgin dakon mai na Switzerland bayan shekara uku da ƙwace shi.
A ranar 12 ga Nuwamba ne hukumomin Najeriya suka ƙwace jirgin sannan suka ajiye shi “nisan tafiyar awa uku zuwa huɗu daga gaɓar ruwa”, a cewar Ms Trehan. Har yanzu fasinjojin na cikin jirgin.
Matar Trehan ta ce sojojin Najeriya suna kulawa game da lafiyar fasinjojin, inda har ma aka yi jinyar mutum biyu da suka kamu da zazzaɓin malariya a cikin jirgin.
Saia dai iyalan mutanen sun ce alaƙar da kawai suke da ita tsakaninsu da su ita ce minti “biyu zuwa uku na kiran waya duk kwana 12 zuwa 15”.
“Ana umartarmu mu yi magana da Ingilishi saboda masu gadinsu su gane abin da muke cewa,” in ji Matilda Sanu, matar Shugaba Sanu Jose.
Matar Trehan ta ce sau uku kacal ta yi magana da mijinta tun watan Nuwamba.
“Mun san cewa kamfanin da ya mallaki jirgin ya samar da abubuwa a kan jirgin,” in ji ta.
“Kwanakin na ƙara yawa. Ba mu san yadda za mu yi ba,” a cewar Sneha Harshvardha, matar Harshvardhan Shouche – wani injiniya da ke cikin jirgin.
“Ba tare da wani laifi da suka aikata ba, ga shi muna ta shan wahala. Ban san yadda zan siffanta tashin hankalin da muke ciki ba,” in ji ta.