
Asalin hoton, Getty Images
Tankar sojojin Rasha kenan da aka lalata a garin Sviatohirsk bayan ƙwace shi
Yaƙin Ukraine da Rasha ta ƙaddamar na shirin shiga shekara ta biyu, tun bayan fara shi.
Mun tattauna da ƙwararru kan harkokin soja da yawa kan yadda suke tunanin lamarin zai kasance a fagen daga cikin sabuwar shekara ta 2023.
Ko za a kai ƙarshensa a sabuwar shekarar, da kuma yadda zai zo ƙarshen – a filin daga ko a teburin sulhu? Ko zai tsallaka zuwa 2024?
‘Hare-haren Rasha a lokacin bazara abu ne muhimmi’
Michael Clark, ƙaramin darakta a cibiyar Strategic Studies Institute, Exeter da ke Birtaniya
Akasarin ƙasashen da suke far wa wata ƙasa da yaƙi a nahiyar Turai kan tsinci kansu a tsakiyar hunturu.
Napoleon, da Hitler, da Stalin dukkansu sai da suka tsahirta a yaƙin da suke yi saboda tsananin sanyin hunturu, shi ma kuma – sakamakon rashin nasara da yake fuskanta – Vladimir Putin na umartar dakarunsa su tsahirta don ƙaddamar da sabbin hare-hare a lokacin bazara.
Duk ɓangarorin biyu na buƙatar tsagaitawa, amma dakarun Ukraine sun fi kayan aiki da kuma ƙwarin gwiwar ci gaba da yaƙin, kuma akwai yiwuwar su ci gaba da dannawar da suke yi, aƙalla ko da a yankin Donbas ne.
Suna gab da ƙwace yankunan Kreminna da Svatove, inda suke ƙoƙarin korar dakarun Rasha zuwa tsawon mil 40 – kusa da inda suka shiga ƙasar a farkon yaƙin daga watan Fabrairu.
Ukraine ba za ta so ta dakata ba daidai lokacin da take ganin ta kusa yin nasara. Amma za su iya tsagaitawa a kudanci bayan sun ƙwace Kherson.
A 2023, babban abin da zai fi muhimmanci shi ne hare-haren Rasha a lokacin bazara.
Putin ya ce sabbin dakarun da aka tattaro kusan 50,000 sun isa filin dagar; sauran 250,000 ɗin na yin atisaye domin shiga a sabuwar shekara.
Babu wani takamaiman abu da za a iya faɗa har sai an ga abin da zai faru da sabbin dakarun na Rasha a fagen daga.
Babu mamaki a samu gajeriyar tsagaita wuta. Sai dai kuma Putin ya ce ba zai dakata ba, ita ma Ukraine ta tabbatar da cewa tana ƙoƙarin ƙwatar kanta ne.
‘Ukraine za ta ƙwato garuruwanta’
Andrei Piontkovsky, ƙwararre kan kimiyya kuma mai sharhi a birnin Washington DC na Amurka
Ukraine za ta yi nasarar ƙwato dukkan garuruwanta da Rasha ta mamaye nan da bazarar 2023. Dalili biyu ne suka sa na ce haka.
Na farko shi ne ƙwarin gwiwa da jajircewa da tunƙahon dakarun Ukraine da ma ƙasar baki ɗayanta, wanda ba a taɓa gani ba a yaƙe-yaƙe na zamanin nan.
Asalin hoton, Reuters
Dakarun Ukraine kenan suke harba makaman atilare a kusa da Bakhmut ranar 26 ga watan Disamba
Na biyun kuma shi ne, bayan shafe shekaru suna ƙoƙarin burge ɗan mulkin kama-karya, ƙasashen Yamma sun fahimci irin sauyin da za a samu nan gaba.
Ana iya gane hakan ta cikin bayanin da Shugaban Ƙungiyar Ƙawance ta Nato, Jens Stoltenberg.
“Asarar da muke yi ta kuɗi ce, yayin da asarar da ‘yan Ukraine ke yi ta jini ce. Idan masu kama-karya suka ga suna yin nasara to asarar da za mu yi nan gaba za ta fi haka girma. Kuma duniya za ta ƙara shiga babban haɗarin yaƙin duniya.”
Takamaiman lokacin da za a kawo ƙarshen yaƙin zai dogara ne kan irin gaggawar da Nato za ta yi wajen aika wa Ukraine makaman kai hari.
Ina ganin garin Melitopol zai zama fagen daga mai muhimmanci a watanni masu zuwa.
Idan suka ƙwace Melitopol, dakarun Ukraine za su tsallaka Kogin Azov cikin sauƙi domin su katse shige da fice zuwa yankin Crimea.
‘Babu alamar tsagaitawa’
Barbara Zanchetta, ta Sashen Nazarin Yaƙi a kwalejin King’s College London
Shugaba Putin na tsammanin Ukraine za ta karɓi buƙatunsa ba tare da jayayyar yaƙi ba, kuma ba tare da saka bakin sauran ƙasashe ba.
Wannan tunanin ya jawo yaƙin da har yanzu babu wata alamar dakatawa.
Lokacin hunturu zai zama mai tsanani saboda hare-haren Rasha da take kaiwa kan kayayyakin more rayuwa domin karya lagon mazauna Ukraine.
Amma kuma ƙwarin gwiwar ‘yan Ukraine a bayyane yake.
Za su ci gaba da jajircewa. Za a ci gaba da yaƙin har illa masha Allahu.
Babu alamun nasara a tattaunawa. Idan har ana son a cimma matsaya to dole fa sai wani ɓangare ya jingine babbar buƙatarsa.
Babu wata alama da ke nuna cewa hakan ta taɓa faruwa ko kuma za ta faru a nan gaba.
Asalin hoton, Getty Images
Ta yaya za a kawo ƙarshen kenan?
Yaƙe-yaƙen da aka yi a baya ta hanyar rashin lissafi kamar na Vietnam da Amurka ta ƙaddamar, ko na Afghanista da Tarayyar Soviet ta yi, sun ƙare ne kawai ta hanyar ficewa daga ƙasashen.
Yanayin siyasa kan sauya a cikin gidan ƙasar da ta kai hari ba tare da cikakken lissafi ba – sai ya zama ko dai su fice cikin girma da arziki ko kuma akasin haka – ficewar ce kaɗai zaɓin da ya rage musu.
‘Babu wani abu illa a doke Rasha’
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Rasha Vladmir Putin lokacin da yake gaishe da Rashawan da suka taru yayin wani biki a birnin Moscow
Ben Hodges, tsohon janar ɗin sojan Amurka a Turai
Ya yi wuri a shirya faretin nasara a birnin Kyiv na Ukraine amma dai su ne ke yin nasara a yanzu kuma babu wata tantama a raina cewa za su yi nasara, babu mamaki a 2023.
Abubuwa za su tsananta a hunturu amma ba wata tantama dakarun Ukraine za su fi jurewa sama da na Rasha saboda kayan sanyi da ake aika musu daga Birtaniya da Canada da Jamus.
Zuwa Janairu, ƙila Ukraine ta shiga zangon ƙarshe na yaƙin, wanda shi ne ƙwato Crimea.
Na yi imanin cewa za a ƙwato Crimea nan da ƙarshen 2023 duk da cewa za a iya cimma wata yarjejeniyar bai wa Rasha lokaci domin kwashe sojan ruwanta daga Sevastopol.
‘Kada a yi tsammanin wani sauyi’
David Gendelman, ƙwararre kan harkokin soja mazaunin Isra’ila
Maimakon batun ta yaya za a kawo ƙarshen yaƙin, ga yadda kowane ɓangare zai so ya cimma muradinsa a zagaye na gaba.
Kusan rabin sabbin dakarun Rasha 300,000 ne ke filin daga a yanzu. Sauran da kuma waɗanda suka fice daga birnin Khaerson za su bai wa Rasha damar kai hare-hare.
Kazalika, akwai yiwuwar ci gaba da salon da ake amfani da shi a yanzu – dannawar dakarun Ukraine ba cikin sauri ba, kamar a Bakhmut da Avdiivka, da kuma ƙila faruwar irin hakan a Svatove-Kreminna.
Za a ci gaba da kai wa kayayyakin Ukraine masu muhimmanci hari.
Su ma dakarun Ukraine da dama sun samu kansu bayan Rasha ta janye daga Kherson.
Dannawa kudanci shi ne abin da ya fi masu domin ƙwato Melitopol ko Berdyansk, da zimmar katse Rasha daga yankin Crimea.
Wannan zai iya zama nasara babba ga Ukraine kuma dalilin da ya sa ke nan Rasha ke ƙara tsaro a Melitopol.
An zaɓi masu sharhin ne saboda ƙwarewa da kuma bambancin ra’ayoyinsu