Hanyoyin da za ku iya fita daga taskun sauyin kuɗi a Najeriya



Jama'a a layin cirar kudi a ATM
Bayanan hoto,

Wasu mutanen har kwana suke yi a layin ATM

Sakamakon halin karancin kuɗi da al’ummar Najeriya, musamman masu ƙaramin ƙarfi suka shiga sanadiyyar sauyin fasalin wasu daga cikin manyan takardun kudin kasar na naira, masana na ganin akwai wasu hanyoyi da ya kamata hukuma da su kansu jama’a su bi domin saukaka halin da aka shiga.

A halin yanzu jama’a kan kwana ko shafe tsawon lokaci a kan layin cirar kuɗi ta na’urar banki wanda kuma duk da haka matsalar na kara ta’azzara.

A tattaunawar da BBC ta yi da Farfesa Muhammad Muttaqa, masanin tattalin arziki a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a Najeriya, yana ganin mataki na farko shi ne, ‘ ya kamata a duba ainahin matsalar a fahimci matakin da kasar take ciki tukuna kafin a ce an bullo da ire-iren wadannan tsare-tsare.‘‘

Masanin ya ce kamata ya yi a tabbatar da cewa kasa tana da wadatacciyar hanyar intanet a yawancin wurare kafin a dauki irin wannan mataki sannan kuma a tabbatar da yawaitar bankuna da kuma ilimi a tsakanin jama’a wanda duka yana ganin babu wadannan tanade-tanade, amma kwatsam gwamnati ta tunkari tsarin.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like