Har Ya Zuwa Wannan Lokaci Kasar Isra’ila Naci Gaba Da Babbakewa



Har yanzu an kasa kashe gobarar da ta kama tun daga ranar Talata a kasar Isra’ila inda a halin yanzu kasashen duniya da dama na aika taimakonsu.
Mai magana da yawun ‘yan sandan kasar Isra’ila Micky Rosenfeld, a halin an yi nasarar shawo kan gobarar a wani yankin kasar inda ake ci gaba da kokarin ganin cewa an kawo karshensa.
A gefe guda kuma labarai daga gidan talebijin Channel 2 na kasar Isra’ila na nuna cewa, gobarar ta sake kama dajin kusa Kudus da kuma garin Hayfa.
A cikin wata rubutacciyar sanarwar da ‘yan sandan Isra’ila ta fitar an ce, an yi nasarar kashe gobarar da ta kama a yankin Kiryat Malahi.
A cikin kasashe da dama sun aika taimako wurin kashe gobarar ciki har da Turkiyya, Amurka, Croatia, Italya, Spaniya, Girka, Falastin, Masar, Jordan da Cypru. Sanarwa ta kuma nuna cewa mutane da dama sun jikkata inda aka yi asarar dukiyoyi.

You may also like