Har yanzu ana cigaba da binciken Lawal da Oke -Magu


Shugaban riko na Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC, Ibrahim Magu ya ce babu wasu shafaffu da mai a yakin da ake da cin hanci da rashawa.

Ya ce, Abdulrashid Maina, tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa kan kudaden fansho, tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal da kuma Ayo Oke tsohon shugaban hukumar leken asiri ta Najeriya NIA har yanzu suna fuskantar bincike.

Magu ya bayyana haka a ranar Talata lokacin a cikin shirin Sun Rise na gidan talabijin din Channels sa’ilin da aka tambaye shi kan ina aka kwana game da laifin wawure kudaden kasa da ake zargin mutanen da yi.

Mai rikon mukamin shugabancin hukumar ta EFCC sai yace “Muna ci gaba da bincike, binciken na cigaba da gudana kuma nan ba da jimawa ba zamu kammala.Ina fada maka babu wani shafaffe da mai a yakin da ake da cin hanci.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like