Har Yanzu Ba A Saji Inda Nmamdi Kanu Ya Boye BaRahotanni sun nuna cewa yanzu kwanaki hudu ke nan ba a san inda Shugaban kungiyar nan ta IPOB, Nnamdi Kanu yake boye ba, haka ma, iyayensa ba a ji duriyarsu ba duk da yake mahaifinsa shi ne Basaraken al’ummar Afaraukwu Ibeku.

Sai dai akwai jita jitar cewa sojoji sun kama iyayen nasa amma kuma Mataimakin Kakakin Rundunar Soja, Sagir Musa ya musanta wannan jita jitar inda ya nuna cewa sojoji ba su tsare Nnamdi Kanu da iyayensa ba.

You may also like