Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya nesanta kansa daga kalaman dake yawo a gari cewa yana goyon bayan takarar shuagaban kasa Muhammad Buhari a karo na biyu.
Obasanjo ya ce bai gana da shugabannin gamayyar kungiyoyin kwadago ba a ranar Talata.
Obasanjo ya kara jaddadawa a cikin sanarwar da ya fitar cewa har yanzu yana kan bakansa bisa kalaman da ya yi cikin wata sanarwa da ya fitar a watan Janairu inda a ciki yake cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari ta kunyata duk wani wanda ya taimaka aka zabe ta.
Obasanjo ya fada batare da shakku ba cikin sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai,Kehinde Akinyemi ya sanyawa hannu cewa bai taba ba kuma ba zai taba goyon bayan rashin nasara ba.
Magoya bayan shugaban kasa Muhammad Buhari sun ta wallafa wasu kalamai musamman a kafafen sadarwar zamani cewa a yanzu Obasanjo ya amince da takarar Buhari a karo na biyu.