Udom Udoma, ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, ya ce har yanzu, shugaban kasa Muhammad Buhari bai karbi rahoton kasafin kudin shekarar 2018 da majalisar kasa ta zartar.
Udoma ya bayyana haka ranar Laraba lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan taron majalisar zartarwar tarayya a fadar shugaban kasa dake Abuja.
A ranar 16 ga watan Mayu majalisar kasa ta amince da kasafin kudin watanni shida bayan da shugaban kasa Muhammad Buhari ya gabatar mata da shi.
Udoma ya ce tsaiko da aka samu na mikawa shugaban kasa kasafin kudin zai kawo illa ga tattalin arzikin kasarnan.
Ya kara da cewa da zarar gwamnatin tarayya ta samu kasafin kudin to zata gaggauta aiki akansa.
“Shugaban kasa bai karbi kasafin kudin ba, saboda haka ba zai yi yu ba ayi magana akan kasafin kudin da ba a riga an karbaba,”ya ce.
Udoma ya kuma musalta maganar da ake yadawa cewa ya ce shugaban kasa ba zai sawa kasafin kudin hannu ba.