Sabanin Rahotanni da ake yayatawa kan cewa Shugaba Buhari ya cire shi daga shugabancin tantance shugabannin gudanarwar hukumomin gwamnati, Sakataren. Gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya jaddada cewa ya kammala aikin da aka dora masa na nauyi na kwamitin kuma tuni ya mika rahotansa ga Shugaba Buhari.
Babachir ya yi bayanin cewa babu yadda zai hada rahoto sannan kuma ya aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahoton ba tare da umarnin Shugaba Buhari ba wanda shi ne ya bashi wannan aiki. Ya ce matakin da Shugaba Buhari ya dauka na mika rahoton ga Mataimakinsa don ci gaba da aikin, ba yana nufin an same shi da wani laifi ba ne.