Har Yanzun Akwai Barazanar Yan Fashin Kan Teku Yan Kasar Somalia


 

Majiyar jami’an tsaro na cikin ruwa ta bayyana cewa akwai barzanar barayin ruwa zasu sace jiragen ruwa masu safara tsakanin tekun Aden da kuma Tekun Arabia hanyar kai kawon jiragen ruwa tsakanin Turai da Asia.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa, a watan da ya gabata wasu barayi cikin ruwa yan kasar Somalia sun yi kokarin sace wani jirgin ruwa dauke da sinadarai a ba tare da samun nasara ba.

Rundunar yaki da satar jiragen ruwa ta tarayyar turai (EU-Navfor) ta tabbatar da wannan labarin ta kuma kara da cewa a ranar 4 ga watan Nuwamba da muke ciki wasu marayin ruwa shidda sun yi kokarin sace wani jirgin ruwa dauke da sinadarai mai suna CPO KOrea 330 a wani wuri kilomita 610 daga gabacin kasar Somalia Sannan a ranar 22 ga watan Octoban da ya gabata ne, a karon farko wasu marayin cikin tekun suka yi kokarin satar wani jirnin ruwa bayan kimani shekara faya da rabi da rashin samun hakan.

Mr North Wood wani tsohon jami’an tsaron Rayal Navy ya fadawa reuters cewa har yanzun akwai barazanar satar jiragen ruwa masu zirga zirga a kan wannan hanyar wacce take daukar kashe 40% da ziraga zirgan juragen ruwa a duniya. Sai dai abin bakin ciki wasu kamfanonin jiragen sun rage matakan tsaron da suke dauka a cikin jiragen nasu bayan dan sararawan da aka sami na kimanin shekara guda da rabi.

You may also like