An Harbe Wata ‘Yar Kunar Bakin Wake a Borno


PIC.10.SOLDIERS ON GUARD ON POST OFFICE ROAD IN MAIDUGURI ON TUESDAY (20/5/14). 3106/20/5/2014/CH/AIN/NAN

 

 

An hallaka ‘yar kunar bakin wake a karamar hukumar Dikwa da ke jahar Borno a lokacin da sojoji suka sakar mata wuta a ranar Lahadin da ta gabata.

‘Yar kunar bakin waken ta yi karyar ita bakuwa ce daga garin Mungono, ta zo ta duba iyayenta a Dikwa. Sai dai sojojin sun gano nufin ta lokacin da suka tuno cewa ba ta bullo ta hanyar gaske ba .

Mai magana da yawun rundunar Kanal Sani Usman ya bayyana cewa yanke hukuncin da sojojin suka yi a lokacin inda suka sakar mata wuta shi ya takaita abun, domin a take bom din ya tashi da ita, al’amarin da ya jikkata jami’an guda uku.

Ya ce wannan al’amari ya nuna cewa har yanzu akwai shingin ‘yan kungiyar ta Boko Haram da ke da nufin haifar da tashin hankali a wasu yankuna.

Ya kara da cewa yawancinsu suna yin basaja ne kamar mahaukata domin su samu shiga wasu bangarorin musammam a jahar Borno.

You may also like