Harbin Bindiga yayin da yan’sanda suka hana yan shi’a shiga harabar majalisar kasa


Ya’yan kungiyar yan uwa Musulmi ta Najeriya da akafi sani da Shi’a sun gwabza da jami’an yan sanda a kofar shiga harabar majalisar ƙasa dake Abuja ranar Litinin.

Sun isa kofar shiga harabar majalisar da tsakar rana amma aka hana su shiga harabar majalisar.

Jami’an tsaro dake gadin kofar sun yi harbin iska lokacin da suke ƙoƙarin tarwatsa su daga wurin. Haka kuma sun yi amfani da barkonon tsakuwa wajen hana su shiga harabar yayin da suka kama wasu daga cikinsu.

Ƙoƙarin tabbatar da yawan mutanen da aka kama ya ci tura yayin da rundunar yan’sandan birnin tarayya Abuja ta gaza fitar da bayani kan abinda yafaru.

Masu zanga-zangar na bukatar a saki shugaban su Ibrahim Elzakzaky wanda ke tsare a hannun jami’an tsaro tun shekarar 2015.

Rikicin na Abuja na zuwa ne kwana guda bayan wani ɗan kungiyar ya rasa ransa a Kaduna lokacin da suke gudanar da wata zanga zanga-zanga makamanciyar wannan.

You may also like