Hare-hare ta sama a Khartoum bayan karyewar yarjejeniyar tsagaita wutacd

Asalin hoton, Getty Images

Faɗa na ci gaba da rincaɓewa a Khartoum babban birnin ƙasar Sudan bayan yin watsi da yarjajeniyar tsagaita wuta domin bai wa fararen damar ficewa daga birnin.

A ranar Lahadi sojojin ƙasar sun ce suna kai wa birnin hare-hare ta kowanne ɓangare ta sama da manyan makaman atilare, domin fatattakar abokan faɗansu dakarun RSF.

Da tsakar daren yau Lahadi ne yarjejeniyar tsagaita wutar ke ƙarewa, yayin da har yanzu miliyoyin mutane ke maƙale a birnin wanda ke fama da ƙarancin abinci.

Tuni dai jirgin farko ɗauke da kayan agaji da magunguna ya isa ƙasar.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like