Hari a Pakistan ya kashe mutane da yawa


Hukumomi da jami’an asibiti a Pakistan sun ce harin bam a wata kasuwar wani yanki na kabilu da ke kan iyar kasar da Afganistan, ya yi sanadiyyar rayukan mutane kusan 20 daura da wasu 35 da suka jikkata.

 

Dr. Sabir Hussain ya shaidar da cewar, ana cigaba da jigilar mutanen da suka jikkata daga kasuwar kayan gwari na Parachinar inda harin ya auku, kuma akasarinsu na cikin hali mawuyaci na jinya.

Jami’in gwamnati Shahid Khan ya bayyana cewar, bam din ya tarwatse ne yayin da kasuwar ta cika makil da mutane da ke sayen kayan gwari daga ‘Yan sari.

Sai dai ya ce ana cigaba da gudanar da bincike dangane da harin, kuma har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhaki.

You may also like