Hari a Mali ya hallaka sojojin Burkina Faso


 

 

Wasu mutane dauke da makamai da ba a san ko suwa ne ba a ranar Juma’an nan sun kai farmaki ga wata cibiya da sojojin kasar Burkina Faso ke zama a kusa da iyakar kasar da Mali.

Burkina Faso Ouagadougou Putsch (Reuters/J. Penney)

Arewacin kasar ta Burkina Faso dai na shan fama da hare-hare na masu ikirarin jihadi daga kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar tun daga shekarar 2015. Harin na wannan Jumma’a 16 ga watan Disambar da muke ciki dai, ya yi sanadi na rayukan sojoji 10 da sanya wuta a wasu gine-gine kamar yadda wata kafar yada labaran wannan kasa da ke a yammacin Afirka ta bayyana.

An dai amince cewa maharan sun shiga sansanin sojojin na Nassoubou a Burkina Faso daga Mali.

You may also like