Hari ta sama ya hallaka mutane 140 dake zaman makoki a Yemen


 

Akwai bukatar gudanar da bincike don gano bangaren da ke da hannu a kazamin harin da aka kai da jiragen yaki  akan masu zaman makoki da ya hallaka rayuka 140 kamar yadda sanarwar da Saudiyya ta fitar yau lahadi ke cewa.

‘Yan tawayen Yemen dai sun zargi jiragen yakin Saudiyya da kawayenta da kai wannan harin da ya hallaka dimbin mutane tare da jikkata wasu fiye da dari biyar a yayin zaman makoki a wani yankin dake a birnin Sana’a.

Sai dai kuma Saudiya da kawayenta da ke fada da ‘Yan tawayen na Huthi a kasar ta Yemen sun musanta zargin kai harin bayan nan ne suka fitar da sanarwar  soma  binciken da zai gano bangaren da ya kai wannan munmunar harin.

A baya dai rundunar kawancen sojin da Saudiyya ke jagoranta sun sha kai harin sama a kan ‘yan Houthi duk da kokarin Majalisar Dinkin Duniya na shirya tattaunawar zaman lafiya da zummar kawon karshen yakin sama da shekaru biyu da ya yi sanadiyar mutuwar dubban rayuka da kuma raba fiye da miliyan daya da matsuguninsu.

Fararren hula sama da dubu hudu ne suka mutu tun bayan soma yaki a Yemen.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like