Hari ya hallaka mutane 14 a Afghansitan


Dan bindiga dadi ya hallaka Musulmai mabiya tafarkin Shia 14 yayin da suke bikin al’ada na shekara-shekara a Afghansitan.

Afghanistan Anschlag in Kabul (Reuters/M. Ismail)

Wani dan bindiga dadi ya hallaka kimanin mutane 14 tare da jikata wasu kusan 40, a wajen da Musulami mabiya tafarkin Shia suke addu’oi da ke birnin Kabul na kasar Afghanistan.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida ya ce lamarin ya faru da yammacin wannan Talata da ta gabata, lokacin da ‘yan Shia suke abubuwan da suka saba na shekar-shekara kan tunawa kisan guilla da aka yi wa Iman Hussein, jika ga Annabi Muhammadu wanda ya kawo addinin Islama.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like