A ƙalla mutane 15 ne suka mutu ya yin da wasu 18 suka jikkata a wasu jerin hare-haren ƙunar ɓakin wake uku da ake zargin ƴaƴan ƙungiyar Boko Haram ne suka kai kasuwar Konduga dake jihar Borno, ranar Juma’a.
Bulama Kaka wani dake kusa da wurin da lamarin yafaru ya fadawa jaridar The Cable cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe da 7 na dare.
Kaka yace ɗaya daga cikin bom ɗin ya fashe yan mitoci kaɗan daga inda yake ya yin da ragowar biyun suka fashe a cikin kasuwar.
Yace wasu daga cikin ƴan kasuwar lamarin ya shafe su.
“Dukkaninmu mun gudu don tsira da rai lokacin da mukaji ƙarar fashewar bom na farko.Mutane da yawa da nasani sun mutu a harin,”yace.
Wani jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ya tabbatarwa da jaridar The Cable faruwar harin, yace waɗanda suka samu ƙananan raunuka na samun kulawa asibitin Konduga.
Ya ƙara da cewa mutanen da suka mutu da kuma wadanda suke cikin wani mawuyacin halin an kai su asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri da kuma babban asibitin Maiduguri.