Wata mota jibge da bama-bamai da aka kai hari da ita kan jami’an tsaro a birnin Benghazi da ke gabashin Libya ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 18, tare da jikkata mutane da dama.
An dai shafe sama da shekara biyu ana gwabza fada tsakanin sojojin kasar da ke samun taimakon kawayensu da kuma kungiyoyin masu tada-kayar-baya da ke mubaya’a ga kungiyar IS.
An dai kai wannnan harin ne bayan kwana guda da jiragen yakin Amurka suka kai hari kan mayakan IS a birnin Sirte.
Wata majiya ta bangaren tsaro a Benghazi ta tabbatar wa BBC cewa an kudiri kai harin bama-baman ne kan hedikwatar ruduna ta 146 ta sojojin Libya, wadanda ke dauki-ba-dadi da kungiyoyin masu tada-kayar-baya a birnin Benghazin.
An dai kashe mutane da dama, mutane da dama kuma sun jikata.
Bama-baman sun tarwatse ne a kusa da wani gidan mai a wata gundumar da ta zama fagen-daga, inda aka yi ta tabka kazamin fada.
Kungiyar masu ta tada-kayar-baya da ke ikirarin juyin-juya-hali ta Benghazi Revolutionary Shura Council ta fito fili ta dauki alhakin kai hari ta hanyar yin bayani a wani dandalin sada zumunta na Twitter da ake dangantawa da kungiyar.
Wannan kungiya dai wani bangare ne na kwambar kungiyoyin masu tada kayar baya a kasar ta Libya da suka yi mubaya’a ga kungiyar IS.
Sun dai gama-kai wuri guda ne domin tunkarar wani gangamin mayakan gwamnati da ke kokarin dakile masu tada kayar baya a kasar, da aka kafa shekaru biyun da suka wuce, wanda kuma ke karkashin jagorancin Janar Khalifa Hefter, .
A wanncan lokacin ana fama da matsalar kisan-gilla a birnin, da kuma hare-haren da ake kaiwa kan sojoji da ‘yan sanda da kuma masu rajin kare hakkin bil’dama kusan a kowace rana.