
Asalin hoton, Getty Images
Wasu hare-haren bam guda biyu da aka kai a tsakiyar lardin Hiraan na Somalia sun hallaka mutum tara na iyali guda.
Wani mataimakin shugaban ƴan sanda na yankin ya ce harin ya kuma kashe ƙarin mutum 26.
Ƙungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaeda ta ɗauki alhakin kai harin.
Kwamishinan yankin Mahas ya ce an yi niyyar kai harin ne a kan gidansa da kuma gidan wani ɗan majalisa.
Magajin garin Mahas, Mumin Mohamed Halane ya shaida wa BBC cewar hari na biyu an kai shi ne a wata kasuwa.
Hare-haren sun yi muni ta yadda ɓaraguzan abubuwan da suka tarwatse suka raunata mutanen da ke da nisa daga inda abin ya faru.
Wani da ya shaida lamarin Adan Hassan ya ce “lamarin ya munana”.
A baya-bayan nan ƙungiyar dakarun gwamnati sun rinƙa samun nasara kan mayakan al-Shabab tun bayan da shugaban ƙasar, Hassan Sheikh Mohmud ya ayyana gagarumin yaƙi a kansu a watan Agusta, bayan harin da suka kai a wani shahararren otal da ke Mogadishu.
Sai dai duk da wahalar da suke sha a hannun dakarun gwamnati, mayaƙan al-Shabab na ci gaba da kai hare-hare a yankin tsakiya da na kudancin Somalia.
Akwai dai dakarun wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afirka da na Amurka waɗanda ke a ƙasar domin taimaka wa gwamnati wurin yaki da ƙungiyar.