Harin Bindiga Ba Zai Hana Mu Yakar Rashawa Ba – Ibrahim Magu


Ibrahim

 

 

Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu ya ce babu abinda zai hana su yakar rashawa komin harin ta’addancin da ‘yan bindiga zasu kai ofishin su

Magu ya bayyana haka ne a wani tattaunawar da yayi da manema labarai bayan harin da ‘yan bindiga suka kai ofishinsu dake babban birnin Abuja. Ya ce harin da ‘yan bindigan suka kai zai kara karfafa musu gwuiwa wajen kwato dukiyar talakawa da barayi gwamnati suka danne.

A jiya ne muka kawo muku rahoton harin da yan bindigan ofishin hukumar dake unguwar Wuse a birnin Abuja inda suka lalata motoci kafin jami’an hukumar su fatatake su.

Ofishin hukumar dake unguwar Wuse ne dai ke kan gaba na binciken laifukan da suka shafi halartar kudaden haramun a karkashin Ishaku Sharu, kuma yanzu haka ofishin na gudanar da bincike kan mutane da dama cikin su harda yan siyasa da ake zargi da aikata irin wadanan laifufuka.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like