Harin Faransa ya kashe mutum 84


160715042615_nice_terror_attack_512x288

 

Hukumomin Faransa sun yi kira da jama’a su bayar da gudunmuwar jini ga mutanen da harin birnin Nice na kasar ya rutsa da su a daren Juma’a.

Kananan yara da dama sun jikkata a harin, kuma an garzaya da su asibitoci domin ba su kulawa.

Iyalai da dama na ci gaba da neman ‘yan uwansu da suka bace.

 

gettyimages-547391970

 

Akalla mutum 84 ne suka mutu harin, wanda aka kai a birnin Nice, a lokacin da wata babbar mota ta kutsa kai cikin taron jama’a da ke bikin ranar samun ‘yancin kai, cikin su kuwa har da kananan yara.

Kimanin mutum hamsin kuma sun jikkata, 18 daga cikin su ke cikin mawuyacin hali.

 

Har safiyar Juma’ar nan ba a iya gano direban motar ba, amma an ga katin shaida na wani matashi dan kasar Faransa wanda kuma dan asalin kasar Tunisiya ne a cikin motar.

Rahotanni sun ce matashin, mai shekara 31 mazaunin birnin na Nice ne, sai dai ba a tabbaatar ba ko shi ne ya kai harin.

Wasu rahotanni sun ce an jiyo karar harbe harbe, ko da dai dama lamarin ya faru ne a lokacin da ake wasa da wuta a wani bangare na bikin na samun yancin kai.

Duniya ta yi tur da harin

Tuni wasu shugabannin kasahen duniya suka yi Allah-Wadai dsa harin.

Kwamitin tsaro na MDD da ya bayyana harin a matsayin wani dabbanci.

Shugaba Obama ya bayyana harin da wani al’amari mai munin gaske inda ya bayyana goyon bayan daukacin Amurkawa da al’ummar Faransa, daddiyar abokiyarta.

Shugaban Majalisar nahiyar turai Donald Tusk, ya ce abun takaici ne harin da aka kaiwa mutane lokacin da suke murnar samun ‘yanci, inda ya ce daukacin al’ummar nahiyar turai dana Asiya na tare da jama’ar Faransa


Like it? Share with your friends!

0

You may also like