Harin Jamus bai da nasaba da IS


Rundunar ‘yansanda Turai ta Europol ba kwakkwarar dangantaka tsakanin IS da matashin nan da ya kai hari kan mutane a wani jirgin kasa a Jamus.

Europol din ta kuma ce haka ma abin ya ke ga harin nan da aka kai a birnin Nice da ke Faransa da Orlando da Florida a Amirka, duk kuwa da cewar wasu daga cikin wadannan mahara sun ce suna da alaka da IS din.

A wani sako da ta fidda, Europol din ta ce bisa ga bayanan da ke gabanta babu wata hujja kwakkwara da ke nuna cewar IS ce ta shirya ta kuma kai wadannan hare-hare tare da taimakon maharan kazalika ba ta samu wata cikakkiyar shaida da ke nuna cewar wasu daga cikin maharan na da alaka ta kai tsaye da IS din ba.

 

You may also like