Harin jiragen yakin Saudiya a yammacin kasar Yemen


4bka09da2e5baeflid_800c450

Jiragen yakin kawancen Saudiya sun kai hari jihar Hadida dake yammacin kasar Yemen

Tashar telbijin din Almayadin dake watsa shirye-shiryenta daga kasar Labnon ta nakalto kafafen yada labaran kasar Yemen na cewa a marecen jiya Alkhamis jiragen yakin kawancen Saudiya sun yi lugudar wuta a yankuna daban daban na jihar Hadida dake yammacin kasar, harin da ya janyo hasara mai yawa ga gine ginen jihar.daga cikin gine gine da harin ya ritsa da su har cibiyoyin tashar ruwan yankin da kuma sansanin Sojin kasar dake bakin ruwa.saidai har ya zuwa yanzu ba bayyana asarar rayukan da wannan hari ya janyo ba.

A bangare guda Mutane 5 ne suka rasa rayukansu a wani  harin Bam na ta’addanci da aka kai  a kusa a garin Ta’az dake kudancin kasar ta Yemen.

Daga lokacin da kasar Saudiya ta fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Al’ummar kasar Yemen bisa fakewar medo da Halarcecciyar Gwamnati ta Shugaba Mansur Hadi da ya yi murabus, shekaru biyu da suka gabata, kungiyoyin ‘yan ta’adda na wahabiyawa masu akidar kafirta Mutane sun fadada kai hare-haren su musaman ma a kudancin kasar.

A nata Bangare kasar Amurka  ta kafa sansanin Sojojin ta a kudancin kasar ta Yemen bisa da’awar yaki da ta’addanci.

You may also like