A kan hanyar Haymana na Ankara babbar birnin kasar Turkiyya wasu ‘yan ta’adda 2 sun tayar da bama-baman da ke daure abin hawarsu, a daidai lokacin ‘yan sanda suka umarce su da mika wuya.
Magajin garin Ankara Ercan Topaca ya ce ‘yan sanda sun yi kacibus da ‘yan ta’addar a wani gidan kiwon dawaki da ke kan hanyar Haymana,sakamakon wani bincike da suka yi a garin Diyarbakir.
An gano ko su waye maharan 2 wadanda suka mutu,kana ana kyautata zaton akwai na ukunsu a boye.
Haka zaika a yayin binciken an gano kilogram 200 na sinadarin amonyum nitrat da wasu ledodi wadanda aka yi mafani da su a wajen hada bama-baman.
Topaca ya ce dalilan da ake da su a yanzu haka na nuna cewa mutanen wadanda ba su yi nasarar kai wa ‘yan sanda da kuma fararen hula hari, da na alaka da kungiyar ta’adda ta PKK.
Daga karshe ya ja hankali al’umar Turkiyya ta su dinka yin taka tsantsan,saboda maharan sun yi shigar burtu tare da daura tutar Turkiyya a abin hawarsu.