Harin kunar bakin wake A Bagadaza


 

Mutane 17 sun rasa rayukansu sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a daidai lokacin da ake gudanar da shagulgulan ranar Ashura a Bagadaza babban birnin kasar Iraki.

‘Yan sandan kasar sun sanar da cewa wani dan ta’adda ne ya tayar bam din da ke daure a jikinsa a a yakin Al Saab.

Abinda ya haifar da mutuwar mutane 17 wasu 50 kuma suka raunana.

You may also like