Harin Mandagali: Gwamnatin Adamawa Na Shirin Hana Sa Hijabi A Wasu WurareBayan harin kunar bakin wajen da aka kai garin Madagali wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akaka mutane 36, gwamnatin Adamawa ta fara nazari kan daukar matakin haramta sanya Hijabi a wasu muhimman wurare.
Da yake karin haske game da batun,  Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Ahmad Sajoh ya ce gwamnati za ta yi aiki da malaman addini wajen cimma matsaya don ganin ba a shiga hurumin addini ba yana mai cewa wasu mata sanye da Hijabi ne suka kai harin kunar bakin waken a ranar Juma’a.

You may also like