Gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin tsaro da su gaggauta tsaurara matakan tsaro a garin Mubi dake jihar Adamawa dama kewayen garin musamman a kasuwanni da guraren ibada.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da, Laolu Akande mai magana da yawunsa ya fitar inda ya ce gwamnati ta kadu ta kuma fusata da harin kunar bakin wajen na ranar Talata kan wani Masallaci da kuma kasuwa a garin na Mubi.
Osinbajo ya ce hukumomin tsaro na aiki tukuru wajen kamo wadanda suke da hannu a harin domin su fuskanci hukunci.
Ya kuma umarci hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da ta gaggauta samar da magunguna isassu da kuma kayan tallafi ga mutanen da lamarin ya rutsa da su.
Ya kuma mika sakon jajensa ga gwamna Bindow,iyalan mutanen da abin ya shafa dama gwamnatin jihar Adamawa.
Mutane sama da 60 ne sai suka rasa rayukansu a harin kunar bakin waken da aka kai garin na Mubi.