Hatsarin jirgin kasa ya kashe mutane 120 a India


 

Ma’aikatan agaji na ci gaba da aikin lalabo masu sauran kwana a wani mummunan hatsarin jirgin kasa da ya auku a jihar Uttar Predash kusa da garin Kanpur a arewacin kasar.

Akalla mutane 120 suka mutu a hatsarin yayin da sama da 200 suka jikkata.

Akwai dai tawagar masu bikin aure daga cikin fasinjan jirgin kasan da ya kauce hanyarsa.

Wannan shi ne hatsari mafi muni a kasar tun hatsarin wani jirgin kasa a 2010 inda mutane 146 suka mututare da jikkata sama 200.

You may also like