Mutane 11 wadanda yawancinsu matane aka tabbatar da sun mutu wasu huɗu kuma suka jikkata bayan wani hatsarin mota da ya rutsa da su a cikin kwaryar birnin Kano ranar Asabar da daddare.
Matan da hatsarin ya rutsa da su suna kan hanyar sune ta dawowa daga Unguwa Uku Yanlemo bayan sun kai amarya inda motar da suke ciki ta kwace ta daki ginin wurin da ake biyan kuɗin amfani da titi dake kusa da Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi.
Matan sun fito ne daga unguwar Hotoro inda akayi bikin kuma aka ɗauki amaryar zuwa unguwar Yanlemo dukkanin unguwannin a cikin birnin Kano.
Mai magana da yawun hukumar kiyaye haɗura ta jihar, Kabir Ibrahim Daura ya ce haɗarin ya faru ne da ƙarfe 8:30 na dare.
Ya ce ” mata 8 ne suka mutu a wurin nan take ɗaya a asibiti biyu kuma a gidajensu. Motar da suke ciki ta rabe biyu bayan da ya daki ginin kuma gudun wuce sa’a ne ya jawo hatsarin duba da irin lalacewar da motar da kuma ginin suka yi.”