Hatsarin mota ya lakume rayukan mutane 12 akan hanyar Lagos zuwa Ibadan


Mutane 12 aka tabbatar da sun mutu ya yin da wasu biyar suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar Lagos zuwa Ibadan.

Hatsarin da ya rutsa da motoci biyu daya ta daukar kaya da kuma wata mota kirar Volvo ta fasinjoji.

Babatunde Akinbiyi, jami’in hulda da jama’a na hukumar tabbatar da bin dokokin hanya ta jihar Ogun, ne ya tabbatarwa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN faruwar lamarin.

Akinbiyi ya kara da cewa hatsarin ya faru ne lokacin da direban motar fasinjojin ya yi kokarin wuce wata mota inda ya yi taho mugama da babbar motar.

Hanyar Lagos zuwa Ibadan na daya daga cikin hanyoyin da ake yawan hatsari wanda ake alakanta shi da gudun wuce sa’a da direbobi suke yi.

You may also like