Hatsarin mota ya rutsa da mutane kungiyar JOHESU 19


Akalla mambobi 19 na hadaddiyar kungiyar ma’aikatan lafiya t JOHESU, sune suka jikkata sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su akan hanyar Auchi zuwa Benin.

Ma’aikatan sun fito ne daga asibitin koyarwa na jami’ar Benin.

A cewar gidan talabijin na Channels ma’aikatan lafiyar su 40 na kan hanyarsu ta halartar wani taro.

Wadanda suka jikkata a lamarin an garzaya da su asibitin Otibho Okhai dake Irrua jihar Edo inda likitoci dake bakin aiki suka yi musu magani.

Esteem Taggar shuagaban kungiyar likitocin gida masu neman kawarewa na asibitin kwararru dake Irrua wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ba a samu asarar rayuka ba a hatsari .

Mambobin kungiyar na cikin wani ya jin aiki da suka fara ranar 17 ga watan Afirilu.

You may also like