Hillary Clinton ta dawo yakin neman zabe


‘Yar takarar shugabancin Amurka ta jam’iyyar Democrat, Hillary Clinton, ta koma fagen yakin neman zabenta, bayan ta da yi jiyyar cutar sanyin hakarkari ta nimoniya (pneumonia).
‘Yar takarar wadda ta gaya wa masu goyon bayanta cewa zaman jiyyar da ta yi a gida ya ba ta damar nazari game da yakin neman zaben nata.

Madam Clinton ta ce tana farin cikin dawowa bakin kamfe din, domin cigaba da gwagwarmayar.

Binciken ra’ayin jama’a ya nuna alamar fafatawa tsakaninta da abokin hamayyarta na jam’iyyar Republican Donald Trump, wanda farin jininsa ga alama ke karuwa bayan da a da ya yi kasa.

Tun da farko Mr Trump ya fitar da wata wasika daga likitansa wadda ke nuna cewa yana da cikakkiyar lafiya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like