Hisbah ta fara binciken matar da ta auri saurayin ƴarta a KanoMata

Asalin hoton, Getty Images

Babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano da ke Najeriya Sheikh Harun Ibn Sina ya shaida wa BBC cewa ya kafa kwamiti domin gudanar da bincike game da zargin da ake yi wa wata mata a jihar na kashe aurenta tare da auren saurayin ƴarta.

Iyayen matar ne dai suka yi ƙorafin cewar shugaban Hisbah na ƙaramar hukumar Rano ya aurar da ƴar tasu ba tare da izininsu ba.

“Kwanaki biyu da suka gabata ne labari ya iso teburina cewa wata mata ta kashe aurenta, inda kuma ta auri saurayin ƴarta, saboda haka nan take na kafa kwamiti domin yin bincike game da batun”.

“Mun gayyato duka ɓangarorin da lamarin ya shafa”.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like