Hotunan Kafin Aure: Ango Ya Saki Amaryar Sa Kwana Daya Da Tarewa


Wani Sabon Ango Mai Suna Jamilu A Karamar Hukumar Dawakin Tofa Dake Jihar Kano ya Saki Sabuwar Amaryarsa Mai Suna Badariyya Akan Laifin Daukar Hoton Kafin Aure (Pre wedding Pictures). Jamilu Wanda Ya Ki Amincewa Da Manema Labarai Su Dauki Muryarsa, Ya Bayyana Cewa Tun Farko Sai Da Ya Hana Ta Yin Hoton Amma Ta Ki.

A Bangaren Amarya Badariyya, Ta Bayyana Cewa, “Ya Hana Ni Yin Hoto Tun Kafin A Daura Auren, Ni Kuma Sai Muka Yi Da Kanin Mahaifiya Ta, Shi Kuma Ya Sa Hoton A Facebook. Shine Da Ya Gani Sai Ya Sake Ni Saki Daya.”

Me Za Ki Ce Akan Wannan Abu Da Ya Faru Gare Ki?

“Ina Ba Wa Mata Shawara Su Daina Yin Abu Idan An Hana Su, Ni Yanzu Ga Abinda Ya Faru Gare Ni”.

MAJIYA: Shirin Baba Suda Na Gidan Rediyon Dala FM, Kano.

You may also like