Hudubar Sallar Juma’ar Tehran : Tir Da Shirun Kasashen Duniya Akan Yakin Yamen


4bk9f6d78a0150ejmp_800c450

 

Tir Da Shirun Kasashen Duniya Da Su ke Shiru Akan Yakin Yamen

Limamin Juma’ar Tehran ya yi tir da shirun da kasashen duniya su ka yi akan laifukan yakin da Saudiyya ta ke yi a Yamen.

Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Kazim Sadiqy, ya yi ishara a cikin hudubarsa ta juma’a da laifukan yakin da Saudiyya ta ke tafkawa a kasar Yamen,musamman kashe kananan yara da kuma harin bayan nan da ta kai a wurin ta’aziyya.

Limamin na Tehran ya kwatanta kisan da Saudiyyar ta ke yi wa kananan yara a Yamen da irin wanda Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta ke yi wa Palasdinawa.

Har ila yau, limamin Tehran din ya ambaci atisayen da sojojin saman Iran su ka yi a karo na 6, sannan ya ce; Sako ne na kawance ga al’ummun wannan yankin, a lokaci daya kuma gargadi ne ga masu adawa da Iran.

You may also like