Hukumar Kwastan ta kama wasu jirage masu saukar Angula da kudinsu ya kai kusa Naira Bilyan biyar wadanda aka shigo da su ba bisa ka’ida ba ta filin saukar jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Shugaban Kwastan na filin saukar jiragen saman, Mista Franka Allanan ya ce har yanzu babu wanda ya gabatar da kansa a matsayin wanda ya mallake su. Wanda a cewarsa, tuni sun mika jiragen ga rundunar Sojan sama na kasa.