Hukumar Alhazan Najeriya Ta Sanar Da Karin Kudin Aikin Hajjin BanaABUJA, NIGERIA – Aikin Hajji na daya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, kuma ana so mutum ya yi akalla sau daya a rayuwarsa, amma saboda bullar cutar Coronavirus ba a yi aikin Hajji ba har tswaon shekaru biyu, daga shekarar 2020 zuwa 2022. Kudin Kujerar aikin Hajji a bara sai da ya kai Naira Miliyan 2.5

Shugaban Hukumar Alhazai Zikirullahi Kunle Hassan ya ce maniyyaci zai biya Naira Miliyan 2.8 kafin ya yi aikin Hajji a bana.

NAHCON CHAIRMAN ZIKIRULLAHI KUNLE HASSAN a taron manema labarai

NAHCON CHAIRMAN ZIKIRULLAHI KUNLE HASSAN a taron manema labarai

Zikirullahi ya ce farashin ya kai nau’i 8 inda jihohin Borno da Yobe ke kan gaba yayin da jihohin Lagos da Ogun suka fi Naira Miliyan 2.9, kenan an samu karin sama da Naira dubu dari uku idan aka kwatanta da kudin da aka biya na aikin hajjin 2022. Zikirullahi ya ce rashin daidaiton farashin ya faru ne saboda jihohin Arewacin kasar sun fi jihohin Kudu kusanci da Saudiyya.

Kwamishinan kula da gudanar da aikin Hajji Abdullahi Magaji Hardawa, ya ce karin ba Najeriya kadai ya shafa ba duk duniya ne, har ma da kasar Saudiyya domin an samu sauyi a farashin canjin dala, kuma kashi 97 cikin dari na kan yadda ake canja Naira zuwa dala ne.

Hardawa ya ce bana an kara wa Najeriya kujerun aikin Hajji zuwa dubu casi’in da biyar, a saboda haka za a samu karin kudade na masaukin alhazai, kuma an kara kudaden haraji a kasar Saudiyya.

Kwamishinan aikin Alhazai na NAHCON ABDULLAHI MAGAJI HARDAWA

Kwamishinan aikin Alhazai na NAHCON ABDULLAHI MAGAJI HARDAWA

Wani abu da ya dauki hankali shi ne cewa hukumar alhazai ta kasa ta ba hukumomin alhazai na jihohi zuwa karshen wannan wata su kawo kudaden alhazansu da suka tanada saboda a samu a kammala shirin jigilar alhazan a kan lokaci.

Mai Aliyu Usman, sakataren hukumar alhazai na jihar Yobe, ya yi tsokaci akan batun inda ya ce wasu dokoki ba na Najeriya ba ne, dokokin Saudiyya ne.

Aliyu ya ce ko me za ka yi sai ka kashe kudi kuma dole a nemi kudi, kama daga jiragen jigila zuwa wurin kwana da kuma abincin da alhazai za su ci, duk kudi ne.

Taron NAHCON na manema labarai akan kudaden Hajjin 2023

Taron NAHCON na manema labarai akan kudaden Hajjin 2023

Ganin cewa bana Najeriya tana da kujeru dubu casa’in da biyar ga kuma karin kudi, ko Najeriyar za ta iya cike gurbin da aka ba ta?

Jami’i a hukumar alhazai ta jihar Sokoto, Shehu Mohammed, ya ce mutane suna da kwadayin zuwa aikin Hajji, saboda haka yana ganin za a cike gurbin da aka ba Najeriya.

Shugaban hukumar alhazai Zikirullahi ya ce kamfanonin jiragen sama da aka amince su yi jigilar maniyyata daga jihohi su ne Air Peace, Azman, Fly Nas, Aero Contractors, da Max Air. Haka kuma an amince da jirage masu zaman kansu guda biyu Arik da Value Jet.

Hukumar alhazan ta kuduri aniyar daukar duk wani dan kasa da ya yi rajistar yin aikin Hajji a bana.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like