Hukumar Bunkasa Yankin Arewa Maso Gabas: Me Ya Sa Akeyi Wa Kano Kyashi Da Hassada? 


Shigar da jihar Kano cikin Jihohin da zasu amfani maikon Hukumar Bunkasa Yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya, ya jawo martani daga wasu tsiraru daga wannan yankin da tayar da kayar baya na yan kungiyar Boko haram ya tagayyara. 

Masu wannan suka dai sun fito karara sun bayyana kyashinsu da rashin hakuri tare da bayyana tsananin hadama suna masu cewar ai Kano bata cikin wannan yanki.

To ni dai a fahimtata duk dan Arewa maso gabashin Nijeriya na halak to yana alfahari da jihar Kano a matsayinta na uwarsa ta biyu, domin Kano ta goya kowa ba tare da nuna bambanci ba. 

A Kano ba a bambacewa tsakanin Babarbare da Bahaushe kowa daya ne, kuma wani abu da ya kamata masu wannan suka su gane shine, an kirkiro wannan hukuma ne domin farfado da yankunan da mayakan Boko Haram suka tagayyara, shin kuna nufin ku ce Kano bata fuskanci wannan matsala ba? Kuma ya kamata masu wannan suka su fahimci cewar Ana iya kafa hukuma irin wannan kuma wani dalili ya sa a shigar da wasu jihohin da basa cikin yankin. 

Misali hukumar NDDC wacce aka yi ta domin al’ummar Neja Delta an shigar da Jihar Abia da Jihar Ondo kuma ban ji ana surutu akai ba. Wani abu da shima ya kamata masu hankali su fahimta shine a duk fadin Nijeriya babu Jihar da ta rungumi ‘yan gudun hijira daga yankin na Arewa maso gabas kamar Kano. 

Allah Ya jikan tsohon gwamnan Kano Kwankwaso ba dan ya mutu ba domin a zamaninsa ya rungumi marayu sama da 100 daga yankin ya dauki nauyinsu na karatu daga asusun al’ummar jihar Kano. 

Ya kamata dai masu wannan suka su sauya tunani. Domin kabilanci da bangaranci ba komai suke nufi ba illa butulci da kyashi .

You may also like