Hukumar DSS ta janye jami’anta dake wurin Saraki da Dogara


Hukumar tsaro ta farin kaya DSS a ranar Lahadi a janye rabin jami’anta da aka tura aiki a wurin shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara.

Hakan na zuwa ne gabanin taron ranar Litinin da za a gudanar tsakanin mataimakin shugaban. Yemi Osinbajo da kuma yan nPDP karkashin jagorancin Yakubu Dogara.

Saraki ya kasance mamba a nPDP wani tsagi na jam’iyar PDP da ya balle a daga jam’iyar a shekarar 2013 inda suka hada karfi da jam’iyar APC domin tunkarar zaben shekarar 2015.

Jaridar The Cable ta gano cewa tuni aka umarci jami’an tsaron dake aiki karkashin mutanen biyu da su kai kansu hedikwatar DSS ba tare da bata lokaci ba.

Babu wani dalili da aka bayar na janye jami’an tsaron sai dai anyi ittifakin cewa fadar shugaban kasa na da hannu a ciki.

Jaridar The Cable ta gaza samun jin tabakin hukumar DSS kasancewar babu mai magana da yawun hukumar tun bayan da Lawal Daura ya karbi ragamar jagorancinta a shekarar 2015.

Amma wasu majiyoyi dake majalisar kasa sun tabbatar da janye jami’an tsaron.

You may also like