Hukumar EFCC Ta Musanta Zargin Gudanar Da Bincike Rashawa Kan Alkalin AlkalaiHukumar EFCC ta musanta rahoton da ake yayatawa  a kafafen Yada Labarai kan cewa Alkalin Alkalai, Mai Shari’a Walter Onnoghen na daga cikin jerin sunayen da hukumar ta fara binciken rashawa a kansu.

Tun da farko dai hukumar ta nuna rashin Jin dadi kan yadda aka fitar da bayanan binciken da take yi a kan wasu manya kasar nan kwanakin kadan bayan ta mika wadannan bayanai ga ma’aikatar Shari’a a bisa bukatar Ministar Shari’a.

Kakakin Hukumar, Wilson Uwujaren ya ce fitar da wadannan bayanai ya gurgunta ayyukan binciken kasancewa ba a jima da fara gudanar da bincike a kan wasu daga cikin mutanen da ake tuhuma ba.

Daga cikin wadanda ake binciken har da Tsohuwar Ministar zamanin mulkin Jonathan, Ngozi Iwaela sai Gwamnan Ekiti, Fayose da kuma Ministan Albarkatun Kasa, Fayemi Kayode ba ya ga kuma wasu tsoffin gwamnoni.

You may also like