Ana zargin Gwamnan da yin gaba da sama da Biliyan 3
Akwai dai laifuffuka sama da 30 a kan wuyan tsohon Gwamnan.
Hukumar EFCC mai yaki da barna a Najeriya ta kara bayyana wasu shaidu a shari’ar ta da tsohon Gwamnan Jihar Abiya wato Orji Uzor Kalu inda ake zargin sa da laifuffuka har guda 34 tun a bara.
Alkali Rotimi Jacobs mai kare Hukumar ya kira shaida na 5 watau wata mata mai suna Toyosi Ekorhi inda aka gabatar da wasu takardun banki domin a karfafa karar.
Tsohon Gwamnan dai tuni yace yana da gaskiya wanda yanzu za a cigaba da shari’a.