Hukumar Hisba Ta Cafke Mabarata 7,751 A Kano



Hukumar Hisba A Kano ta cafke Mabarata har 7,751 sakamakon karyar dokar da ta haramta barace barace a kan manyan titinan birnin.

Kakakin Hukumar, Malam Umar Yahaya ya ce, dokar ta fara aiki ne tun daga watan Janairu na wannan shekarar inda ya nuna cewa daga cikin wadanda aka cafke akwai kananan yara har 2,476 sauran kuma duk sun manyanta.

You may also like